Kamfanin Google, yayi alkawarin kawo canji ga sakamakon da ke fitowa cikin shafin bincikensa dake kan yanar gizo, da kuma hukunta duk shafukan yanar gizon da aka samu da laifin yada akidoji marasa kyau da kuma labaran ‘kanzon kurege.
Google, ya ce zai rage darajar shafukan yanar gizo da ya samu da rashin inganci, ya kuma baiwa mutane damar bayar da rahotan duk wani shafi da suka samu ‘dauke da wani abin da bai kamata ba lokacin da suke bincike.
Wannan mataki da Google, ya ‘dauka ya biyo bayan matsin lamba da ya yi ta fuskanta a ‘yan watannin da suka gabata, kan cewar yana da hannu wajen yada labaran ‘karya da kuma zaci-fadi a shafin bincikensa kan yanar gizo.
Shi dai shafin binciken na yanar gizo, wanda ke aiki da wata na’urar kwamfuta da ke tantance labaran ‘karya da na gaskiya, wadda wasu lokutan takan kasa banbance labaran, hakan yasa mutane kan samu jerin labaran ‘karya a sakamakon binciken da suka yi a shafin Google.
Google dai ya ce ya ‘dauki wasu tawagar kwararru aiki, wadanda zasu binciki wannan lamari da kuma sake duba na’urar da ke wannan aiki.
Wannan canji dai na zuwa ne bayan da aka samu wani shafin yanar gizo, ciki harda shafukan da ke karyata labarin kashe yahudawa da kuma wanda ke ikirarin tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya na shirya juyin mulki a fadar White House.