Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamna Baida Hurumin Hana Shi


Dr. Babangida Aliyu
Dr. Babangida Aliyu

Mataimakin Gwamna jihar Neja, Ahmed Musa Ibeto, yace Gwamna jihar Dr. Mua’zu Babangida Aliyu, ne ya tursassa shi fita daga taron majalisar zartarwar jihar.

Mataimakin Gwamnan dai yana maida martani ne, a kan wata sanarwar da aka fitar daga gidan Gwamnatin jihar, mai dauke da sa hannun kakakin Gwamna Mr.Israel Ibije, dake nuna cewa shi mataimakin Gwamnan ne ya nemi a saukake masa daga halartar taron majalisar zartarwar jihar.

Musa Ibeto, yace “ Hakikanin gaskiya, Gwamna Babangida Aliyu, ne ya taso da maganar cewa ba zai yu in zauna a cikinsu ba yayin da suke zartar da abubuwa na majalisar zartarwar jiha ba, domin ni ba dan jam’iyyar PDP bane, amma har yanzu inna matsayin mataimakin Gwamna.”

Wani Lauya, Abdulmalik Sarkin Daji, yayi mana Karin bayani, yana mai cewa Gwamna Babangida Aliyu, shine shugaban majalisar zartarwar jihar, amma bashi da hurumin hana mataimakin Gwamna, halartar majalisar zartarwar jihar.

Gwamnan Jihar Neja - 3'18"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00

XS
SM
MD
LG