WASHINGTON DC —
Gwamna jihar Uyo, Udom Emmanuel ya bada umarni a rufe kimani makarantu masu zaman kansu saba’in da takwas (78) da suka hada da makarantar rainon yara dana firamari da kuma na sakandare.
Babbar sakatariyar ma’aikatar Ilimi na jihar Mrs. Valarie Obot, ta ce dokar rufe makarantun ya fara aiki ne tun ranar 4 ga watan Satumba 2017.
Dokar rufe ,makarantun ya shafe makarantun dare da cibiyoyin da ake daukar darusan jarabawan JAMB, wadanda basu samu amincewa gwamnati ba a koina a fadin jihar ta Akwa Ibom.
Tun farko kwamishinan Ilimi, na jihar ya nemi wadannan makarantu dasu daidaita matsayin makarantun su da ma’aikatar ilimi jihar kafin karshen watan Agustan da ya gabata kamar yadda dokar ta tanada amma basu yi hakan ba.
Facebook Forum