Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Kasar Singapore na Shirin Kera Motoci Masu Tuka Kansu


Mr. Pang Kin Keong, babban sakataren ma’aikatar sufurin kasar Singapore, na tunanin gina kasaitaccen birni inda ko’ina zai kasance tsab kuma mutane na shiga motoci masu tuka kansu.

Gwamnatin kasar Singapore na son gina birni mara tituna da yawa, don samun sararin gina wuraren hutawa da kuma damar samar da karin hanyoyin jigilar mutane ta yin amfani da motoci masu tuka kansu. Singapore na son gina titunan mota na karkashin kasa kuma za ta yi amfani da wani dan kumbon hawa don kai mutane wurare dabam-dabam daga tashar ta karkashin kasa.

A wata hira da aka yi da shi a ofishinsa, Mr. Pan ya ce ya zama dole Dan Adam ya kasance cikin tunani da nazarin abubuwa.

Daga yankin Silicon Valley na arewacin jihar California dake Amurka zuwa kudancin kasar Austria, kamfanoni na ta fafutikar ganin sun sarrafa motoci masu tuka kansu. Amma abin da ya sha-bambam da na kasar Singapore shine, gwamnatin kasar ce ta samar da kudaden gudanar da bincike kuma tana son ta yi amfani da motocin (masu tuka kansu) don jigilar jama’a (haya).

Idan har kasar Singapore ta yi nasarar cimma burinta na kera motoci masu sarrafa kansu, tabbasa kasashen duniya za su bi sahun fasaharsu.

XS
SM
MD
LG