A kowane lokaci yakamata ace matasa su zama masu tunani don kirkiro wata hanya da zasu samarma kansu abunyi, yafi kamata ace kowane mahaluki yayi amfani da basira da baiwa da Allah yabashi wajen fito da wata hanya da mutane zasu amfana da wasunsu.
Malama Aziza, wata matashiyace me sana’ar gyaran jiki ga mata, wannan sana’ar da takeyi wata hanyace da take taimakama mata don su zamo masu kokarin jawo hankullan mazajensu daga kallon wasu mata a waje.
Ita dai akanzo gidan ta kuma takan maida tsohuwa yarinya ta yadda mazajen su zasu dinga sha’awar su a kowane lokaci, kuma takan basu wasu sunadarai da zasu sha don gyaran jiki.
Ta fara wannan sna’ar ce shekaru da dama da suka wuce, kuma tana kira ga ‘yan’uwanta mata da su tashi tsaye wajen neman nakansu, don ba’a san mata da ragwanci ba ko kasalan jiki. Sabo da ta haka ne kawai suma zasu zama cikin masu bada tasu gudunmawa ga cigaban kasa.