Mai horas da ‘yan wasan kasar Amurka Jurgen Klinsmann ya ce ya shirya tsaf domin ya jijjiga kungiyar kwallon kafa ta kasar Argentina a wasan da zasu buga na ranar laraba 22 ga watan yunin da muke ciki.
kamar yadda babban kocin ya ce bai damu da ganin Lionel Messi a gaban sa ba domin kuwa a shekarun baya da suka gabata ya kara da kungiyar kwallon kafa ta Portugal wadda Cristiano Renaldo na ciki kuma ya sha su kwallaye biyu da nema.
A bangaren saye da sayarwa kuma, kungiyar Manchester City sun shiga sahun kungiyar kwallon kafa da Barcelona wajan neman fitaccen dan wasan nan mai shekaru 29 da haihuwa Lolita akan kudi fan miliyan 14.
Fernando Torres kuma ya sake rattaba hannu a kungiyar sa ta Atletico Madrid dake kasar Spain har na tsawon shekara guda.