Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada-hadar Kasuwanci Da Zawarcin Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


Kungiyar kwallon kafa ta Man Utd, tace sunyi kusan cimma daidaitawa da Juventus domin sayen dan wasanta Paul Pogba, akan kudi yuro milyan €105, inda zai iya zamowa dan wasan da yafi kowane dan wasan kwallon kafa a duniya tsada a yanzu haka, cinikin da aka dade ana yinsa kuma ya dauki hankalin duk wani mai shi’awar kwallon kafa a duniya.

A gefe guda kuwa, wasu masu horas da ‘yan wasan kwallon kafa irin su Wenger na Arsenal da kocin Liverpool, suna ganin wannan ciniki bai dace ba kuma a ganin su zai iya zamowa kamar asara ce sayen dan wasa da tsada haka daga lokacin da yasamu rauni zai iya kasancewa bashi da amfani.

Ta dalilin haka ne suka nuna cewa gara a sayi mutane uku masu karamin kudi domin rage yiwuwar asarar da ka iya gittawa.

Shi dai Paul pogba ya bar kungiyar Man Utd a shekara ta 2012, zuwa kungiyar Juventus, kyauta a lokacin Sir Alex Ferguson yana manajan kungiyar ta Man Utd.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG