A karon farko, yawan mutanen dake yin amfani da shafin sada zumunci na Facebook a kan intanet, ya kai mutane miliyan dubu daya a kowace rana. Wannan dai bai bayar da mamaki ba ganin cewa babu wani shafin intanet mai farin jinin Facebook a yanzu haka, domin ya zamo tamkar wani bangare na rayuwa. Muna dogaro da Facebook domin jin labaran ‘yan’uwa da abokan arziki na nesa da kusa, ko jin labaran abubuwan dake wakana a duniya, ko yin hulda da abokan da muka rabu da gani shekaru aru aru da suka shige.
Amma duk da yawan yin amfani da wannan shafi na Facebook, tana yiwuwa akwai wasu abubuwa masu sauki da mutum bai sani ba, wadanda kuma zasu iya kyautata yadda zai ji dadi da kuma saukin amfani da wannan shafi na Facebook. Daga yau, DandalinVOA zai fara kawo muku bayanan wasu dabaru guda 10 da zasu iya kawo muku saukin amfani da Facebook.
Yadda Zaka Kayyade Wadanda Zasu Iya Ganin APPS Da kake Amfani Da Su:
Idan kana shiga Facebook ta wasu APPS kamar Spotify ko Candy Crush, to lallai abokanka na Facebook zasu rika ganin dukkan abubuwan da kake yi a wannan shafi cikin labaran da yake tura musu, zasu ga irin wakokin da kake ji, ko sau nawa kake ji da lokutan da kake ji, da dai sauran bayananka da watakila ba kowa ne cikin jerin abokan naka na Facebook zaka so su gani ba. Amma idan ka ga dama, kana iya saukaka ma kanka ta hanyar hana irin wadannan APPS tura ma abokanka bayanin duk wani abinda kayi.
Ga irin matakan da zaka dauka:
Na farko, ka shiga shafin Facebook ta amfani da Browser, amma a kan kwamfuta. Yi a kan kwamfuta din ya fi sauki, amma idan b aka da ita, kana iya budewa a wayarka, ka bude browser na wayarka, kaje shafin Facebook. Idan ka shiga a waya, sai ka duba a kasa inda aka rubuta “View Full Site” ka matsa wannan.
A gefen hagu a shafin, zaka ga inda aka sanya APPS, idan ka kai abin nuni na kwamfuta jiki, zai nuna maka inda aka rubuta “MORE” watau karin bayani game da APPS da kake amfani da su. Sai ka matsa wannan inda aka rubuta “MORE”
Daga nan sai ka zabi inda aka rubuta “SETTINGS”. Idan kayi haka, to zaka ga dukkan APPS da suke kunne a shafinka na Facebook.
Idan kana son rufewa ko toshe wani APP, sai ka kai manuniyar kwamfuta kan wannan APP din zaka ga alamar Fensir ya fito, sai ka matsa wannan alama ta Fensir din.
Idan ka matsa fensir din zai bude maka jerin wasu abubuwan da shi wannan APP zai iya yi a shafinka na Facebook tare da b aka damar zaben abinda b aka son yayi.
Daya daga cikin abubuwan da zaka iya yi ma tarnaki, shine inda aka rubuta “APP VISIBILITY” watau inda zaka iya takaita wanda zai iya ganin abinda kake yi da wannan APP a shafinka na Facebook.
Idan ka matsa APP VISIBILITY, sai ka zabi inda aka ce “ONLY ME” watau kai kadai zaka iya ganin abinda kake yi da wannan APP.
Idan ka matsa shi, to babu wani wanda zai iya ganin duk wani abu da ya shafi wannan APP a cikin jerin abokanka na Facebook. Idan kana son wani takamammen mutum ne ko wasu su rika gani, shi ma kana iya zaben inda aka rubuta CUSTOM, ka sanya sunayen wadanda kake son suna gani, ko ka rubuta sunayen wadanda b aka so suna gani.
A kashi na biyu a gaba, zamu yi bayanin yadda mutum zai iya toshe sakonnin nan da wani lokaci suke ta zuwa cewa abokinka kaza ya na so kayi wannan wasa ko game a facebook da makamantansu.