Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harshe Da Karin Maganar Bahaushe


Kantar Littattafan Tarihi
Kantar Littattafan Tarihi

Shin ina asalin karin maganar Bahaushe da kuma alakarsa da harshen Hausa din? Ina asali kalmomin Hausa ke fitowa ne? Misalin Bazawara ko Saurayi da makamantansu.

Wakiliyar Muryar Amurka Baraka Bashir daga Kano ta hada mana rahoton tarihin harshe da Karin maganar Bahaushe. Inda ta sami zantawa da Dakta Abdullahi Garba Imam na Kwalejin Koyon Shari’a ta Kano.

Malamin ya bayyana cewa ba wanda zai iya tantance lokacin da Bahaushen ya fara Karin magana domin kuwa Karin magana ya faro ne daga ranar da aka fara amfani da harshe, sai dai akan sami karuwar karin magana a kullum sannan adon magana ne don kar a ginshi jama’a.

Daktan bai tsaya nan ba sai da ya kawo mana maganar bahaushe ta al’adar zance da kuma samartaka. Ya bada misalin asalin yadda aka sami kalmar Bazawara da kuma Kalmar Saurayi a sahun samartaka. Kama tun daga wadda ta taba aure har zuwa wacce bata taba auren ba.

XS
SM
MD
LG