Ina matasa masu anfani da kafar sadarwar yanar gizo domin aikata mugayen laifuka? wannan sako ne na musamman a cewar wani jami'in 'yan sanda wanda ake biya makudan kudade domin ya sa ido musamman akan masu anfani da manhajar INSTAGRAM.
Jami'in ya bada bayanin cewa "lallai wannan manhaja ta instagram tana taimaka mana wajan kama mutane masu aikata laifuka da dama, sukan lika hotunan su, wani lokacin ma harda irin mugayen ayyukan da suke aikatawa kuma wasu ma har suna bugun kirji da shi".
A cewar mai magana da yawun 'yan sandan mr Albie Esparza, suna samun bayanai ingantattu ta wannan hanya kuma ya bada misalin wani matashi dan shekaru 17, wanda ya ke anfani da suna "40glock" kuma aka caje shi da mallakar makami ba bisa ka'ida ba.
Yawancin matasa dai suna lika hotunan su akan wannan shafi domin sada zumnci da samartaka a tsakanin su, kuma wasu da dama suna anfani dsa ita domin danfara da sauran laifuka makamantan su.
Dan haka matasa ayi hattara domin duk hoton da aka lika a akan wannan shafi, ana iya ganin shi kuma za'a iya anfani da shi domin gano wanda ya lika hoton a duk inda ya ke.