Reshen majalisar dinkin duniya mai kula da tallafawa bakin haure a jamhuriyar Nijar, yana bada horo ga bakin haure daga kasashen yammacin Afirka daban daban dake neman tsallakawa zuwa arewacin Afirka inda daga nan suke neman hanya zuwa kasashen turai, da kuma matasa marasa ayyukan yi sana’o’in hannu domin dogaro da kai koda sun koma kasashen su.
Ana gudanar da wannan horo ne a cibiyoyi guda uku dake cikin Agadez, Malam Azama Muhamman shine jami’in dake kula da harkokin bakin haure, kuma yayi wa wakilin sashen Hausa na muryar Amurka Haruna Mamman Bako bayanin cewa sun bullo da sabon shirinne domin taimakawa matafiyan komawa kasashen su da abinda zasu iya dogaro akai.
Jami’in ya bayyana cewa akwai matasa da dama daga jihar wadanda suka gama makaranta amma babu ayyukan yi, da kuma wadanda suka fita ba tare da sun kammala karatu ba, duk a cibiyoyin horaswar domin koyon sana’o’in hannu.
Ana sa ran horon zai taimaka wajan rage yawan tafiye tafiye masu hadurran gaske da matasan kan yi wanda ke hallaka daruruwa da dama a hamada ko a Teku yayin da suke kokarin ketarawa.
Matasan da suka ci moriyar shirin sun bayyana jin dadin su, da kuma yin godiya ga majalisar dinkin duniya da gwamnatin kasar musamman akan hanyar dogaro da kai da aka dora su. Matasa hamsinne shirin ya fara horaswa akan sana’ar kira.