Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ina Nasabar Dabi'ar Zuwa Shopping Da Samari Ke Kai 'Yan Mata Da Al'adar Hausa


A wannan karon mun nemi jin ra'ayoyin samari ne musamman akan sabuwar dabi'ar nan da suka dorawa kansu wato daukar 'yan mata zuwa shopping, woto sayyayya a manyan kantuna ko super market a turance.

Wannan ala'ada dai bakuwa ce a al'adar Hausa, amma saboda shigowar zamani dayawa samari da 'yan mata kan yi tattaki zuwa manyan kantuna domin sayen wasu abubuwa musamman domin nunawa juna kauna a cewar wasu samari.

Sai dai kuma da dama sun nuna cewar tasirin wannan harka yafi aminci idan saurayin yana da abin hawa. koda shike wasu kan dauki hayar abin hawan ko kuma su taka a kasa idan wurin bashi da nisa kwarai.

Samari dai a cewar wasu da dama sun lura cewar yawanci duk lokacin da ya kasance saurayi ya dauki budurwa zawa shopping, takan koma ta ba kawayenta labarin irin kula da kuma nuna zamananci da saurayin ta ya nuna mata. Sai dai kuma mai iyaye suke cewa? ku biyo mu domin jin ta bakin iyayen dangane da wannan lamari.

Ga cikakkiyar hirar.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG