WASHINGTON, DC —
A shirinmu na nishadi a yau ma ,na mussamam ne domin mun lalubo jarumi Ibraim Mai-shinku wanda masu kallo suka shafe tsawon lokaci basa ganinsa a akwatin talabijin dinsu.
Ibahim Mai-shinku ya ce yana nan daram yanayi ne na rayuwa amma ya dawo a shiryensa domin fito da wasu fina-finai masu kayatarwa da fadarkawa domin nishadantarwa da ilimantar da jama'a.
Ya ce a tsawon lokacin da yayi ba’a ganinsa a akwatin talabijin ya je neman ilimi ne domin ya inganta harkar sa ta fim, ya kara da cewa a yanzu ma'abota fina finai zasu ga ingantattun fina finai daidai da zamani.
A fannin tsegumi kuwa jarumai masu tasowa ,yan tagwaye Hasana da Husaina Musa sun dawo daga jihar Imo inda suka je bisa gayyatar gwamna Rochas Okorocha ya yi musu.