Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Inna Tabbatar wa Kaina da Kuma Duniya Cewa Haka ne


Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

Yayin da a ciki da wajen Najeriya, ake cigaba da maida martini game da dage babban zabe, masana harkar tsaron a Najeriya, sun bukaci shuwagabanin hukumomin tsaro da suyi murabus, sakamakon matakin da suka dauka na cewa bazasu iya tabbatar da tsaro ba yayin zaben, dalilin da yasa hukumar zaben kasar { INEC} ta dage zaben.

Dr. Bawa Abdullahi Wase, wani masanin harkokin tsaron ne ya furta haka a wata hira da wakilin muryar Amurka, Ibrahim Abdulazeez, yana mai cewa Sojojin Najeriya, sun baiwa Najeriya, kunya.

Ya kara da cewa “An siyasantar da aikin Soja, an siyasantar da kwamandojin Soja, dalilin da kennan yanzu ake amfani dasu, a kuma bisa da dalilin, da suka bayar, idan a kasa ne wadda akwai shuwagabani na kwarai, da a lokacin da jami’an tsaro suka ce su bazasu iya kare wani abuda ya shafi wannan bangare na zabe ba, toh da daga jiya yakamata, duk suyi murabus, idan kuma ba suyi murabus ba, da daga jiya din yakamata duk a sallamesu, bayan sallamar su kuma a tuhumesu da cin ammanar kasa, saboda kowane daga cikinsu sai da ya yantse cewa zai tsare kasa batare da kula da addini, ko bangare ko yare ba, amma abunda jami’an tsaro suka fada, cin ammanar kasa ne, kuma inna tabbatar wa kaina da kuma duniya, cewa haka ne yadda mu a bangaren tsaro muke kallon abun kennan.”

Dr. Wase, ya kuma bukaci ‘yan adawa, da kada su tada hakali a wannan abun, domin duniya yanzu ta gane cewa jami’an dake mulki a yanzu sun ga alamun zasu fadi zabe.

Jami'an Tsaron Najeriya -3'44"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00

XS
SM
MD
LG