Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iyaye na Suka sa Zan Kashe Kai na


Mata Iyaye!
Mata Iyaye!

Wani babban abu me matukar mahimanci a rayuwa yau da kullun, musamman ta yara mata matasa itace, uwaye su kokarta su jawo ‘yayan su a jika don sasu a hanya da ta kamata. Ta yin haka ne kawai zaka ga cewar yara kanbi koyarwa da shawarar iyayen su a duk lokacin da suka zamo mutane.

Wata yarinya Hafsat Hussaini, da iyayen ta suka hanata auren masoyinta ta nemi hallaka kanta, da madarar fiya fiya, wanda dai Allah yasa tana da sauran kwana a gaba. Ita dai wannan yarinyar ta gayama iyayenta aure take so, amma iyayen nata sukace karatu suke so tayi, amma wannan yarinyar bata gamsu da shawarar iyayenta ba.

Sabo da iyayen ta sunce basu aminta da tarbiyar mijin da ta kawo ba, saboda shi direban babbar motane, ita dai taga cewar da dai a hanamata masoyinta to gara ta mutu suma iyayen nata su hutu. Amma a tabakin mahaifin Hafsat Malam Hussaini, yace shi baya hanata aurenshi bane kawai shi dai ya bata shawar kancewar ta duba ta ga yayunta biyu sun auri direbobin mota wanda daga bisani mazajen suka barsu da cuta me karya garkuwan jiki, wanda suka barsu da ‘yaya da yawa.

Don wannan dalilin ne yasa yake gani bai kamata ace ta auri wani me irin wannan sana’ar ba don basu da kamu kai irin wadannan mutane. Kuma shi ba zai so ace ya sake bada ‘yarshi a hannun wani wanda bai aminta da tarbiyarshi ba.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG