Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jawabin Dr Mai Kano Madaki Sa Hannun Maza A Ayyukan Gida


Zamantakewa tsakanin miji da mata ta samo asali tarihij duniya, kuma zamantakewa ce mai matukar muhimmanci wadda take cike da albarkatu iri iri, kama daga 'ya 'ya zuwa sauran abubuwan da jama'a da dama ke cin moriyar su a rayuwa.

Kamar yadda bakon namu na yau wato Dr mai Kano Abdullahi daga jami'ar Bayero dake jahar Kano wanda ya kware a fanin asnin halaiyya da zamantakrewa dan adam, malamin ya bayyana, zaman takewa tsakanin miji da mata ta wuce mizanin da za a ce wata bukata ta taso amma daya daga ciki zai zauna yana kallo bai taimaka ba.

A cewar sa, ba abin kunya bane idan namiji ya taimaka wa matar sa wajan aiwatar da wasu ayyuka cikin gida, ya kara da cewa yin hakan zai haifar da sakamako mai nagari domin yana nuna kauna.

Da muka nemi jin ta bakin kwararren malamin dangane da ra'ayoyin wasu na cewa yin hakan yakan kawo raini, malamin ya bayyana mana cewa babu yadda za'ayi abin kirki ya zama na tsiya, wato raini kan shiga tsakani ne idan mutum ya zubda mutuncin sa.

Ga cikakkiyra hirar.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG