Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kaciyar Mata Yanka Batare da ILimin Halittun Dake Wurin ba.


Wasu mata
Wasu mata

A Kasashen Afirka, fiye da yara miliyan dari da shekarun su bai wuce goma sha biyar ba dama wadanda ke kasa da haka aka fi yiwa kaciyar mata.

Haka ma fiye da mata manya da kanana milyan dari da arba’in, a duk duniya ke dauke da matsalolin dake tattare da kaciyar ta mata.

Yawancin masu magungunar gargajiya ne suka fi taka mahimmiyar rawa wajen gudanar da kaciyar ta mata, a lokacin da suke yara.

Wani Likita akan harkokin mata a asibitin Malam Aminu Kano, Dr. Idris Sulaiman Abubakar, yace babban matsalar kaciyar mata alokacin da ake yi ko kuma idan an gama shine zubarda jini, saboda yanka ne ake yi batare da sanin ilimin halittun da suke gurin ba.

Ya kara da cewa kwayoyin cuta na iya shiga cikin inda aka yi yankan ya zama cewar haihuwa ya zama da wuya koda ta samu tayi aure.

Kaciyar Mata - 2'14"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:14 0:00

XS
SM
MD
LG