Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kada A Zubar Da Shara Ko Ina


A yayin da daukacin musulmi ke bukukuwan sallah a fadin duniya, babban sakatare na ma'aikatar kula da muhalli ta jahar Legas Oluwatoyin Onisarotu ya fitar da wata sanarwa da kuma shawarwari ga daukacin jama'ar jahar legas da cewar su yi bukukuwan sallah cikin zaman lumana da kwanciyar hankali da kuma kula da tsabtace muhalli.

A sanarwar, babban sakataren ya yi kira da cewar yakamata jama'a su yi amfani da abubuwan tara shara da kuma kiyaye zubar da shara a ko ina, domin saukaka kwasar sharar daga maaikatan kwasar sharan.

Ya kara da cewa, dukkana jama'ar legas su sa hannu wajan taya gwamnatin jahar kula da kuma tsabtace muhalli domin inganta kiwon lafiya da tattalin arziki da walwalar jama'ar jahar baki daya.

Har ila yau ya kara da cewa damina bata kaiga wucewa ba, dan haka ana iya fuskantar matasalar ambaliyar ruwa a jahar duk da shike an kwana biyu ba'a sami afkuwar irin wannan matasalar a jahar ba.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG