Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ka’idoji Kafin Zama Jarumi Ko Jaruma A Fina Finan Hausa


Jarumin Fina-Finan Hausa, Ali Nuhu
Jarumin Fina-Finan Hausa, Ali Nuhu

Shirin Nishadi ya sami zantawa da Falalu A. Doraya, wani jigo mai shiryawa da rubuta fina finai kuma mai bada umarni, wakiliyar Dandali Baraka Bashir ta tambayeshi ko me ya ja hankalinsa ga wannan harka.

Falalu dai ya ce yayi shekara ashirin da biyu cikin wannan masana’antar fina finan Hausa, ya kuma bayyana mana kafin ya fara wannan harkar yace wasa irin na Dandali da ake kira stage drama shine ke gabansa, domin da shi ya fara kuma ya ja ra’ayinsa ga shiga harkar fina finai.

Alokacin da aka tambayeshi yadda suke tantance jaruma ko jaruma kafin shiga wasan fim, Falalu dai yace ba producer ko mai shirya fina finai bane ke dauka ba, domin akwai mutane da suke biyowa ta hannun su amma suna gaya musu cewa basu ke dauka ba kungiya ce, ita kanta kungiyar dai tana da wasu ka’idoji da sai mutum ya cika su kafin ya zama Jarumi ko Jaruma.

Da farko dai kungiya zata fara da duba waye mahaifinka ko wacece mahaifiyarka, an kuma fi yadda da yayye maza kasancewar su suka fi zafi a gida, to dole sai daya daga cikin magabata yayi maka jagoranci kafin kungiya ta baka damar shiga wasannin fina finai. Duk wannan kuwa ya biyo bayan yarfe da cin zarafi da aka fuskanta a baya shiysa kungiyar ta karfafa wannan ka’idoji tun shekara ta 2005.

Saurari cikakkiyar hirar.

XS
SM
MD
LG