Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kalubalen Da Dalibai Ke Fuskanta A Jami'oi


Nawar Usman
Nawar Usman

Nawar Usman wata matashiya ta ce Babban kalubalen da dalibai ke fuskantar a jami’a, shine rashin dakin kwana, abubuwan dake shiwa daliban tuwo a kwarya. Sun hada da rashin malamai a ajujuwasu a wasu lokuta.

Ta ce a lokacin da ta zana jarrabawa shiga jami’a na JAMB ta so ta karanci aikin likitanci amma hakkar ta bata cimma ruwa ba inda daga bisani aka bata gurbin karantar Biology, watau ilimin kimiya sanin halirtan dan Adam, wanda a shi ta kammala digiri dinta.

Nawar ta ce zirga zirga daga waje zuwa makaranta a kullum na daga cikin babban abinda ke kawo dalibai chikas bayan ga fadi tashi na karatu na yau da kullum.

Ta ce ko da yake a yanzu tana son abinda ta karanta , kuma tana da burin kammala karatunta na digiri na biyu, kafin ta fara aikinta na koyarwa. Ta kara da cewa tana son aikin koyarwa ne domin itama tana son ta bada nata gudumawa wajan ilimantar da ‘yan baya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

XS
SM
MD
LG