Nishadi tare da Mal Bosho
A yau dandalinVOA ya samu bakwanci jarumi kuma sarkin raha Suleman Yahaya Hamma wanda aka fi sani da malam Bosho ,wanda ya shafe shekaru talatin da biyar yana hakar fim.
Ya ce ya tsince kansa a harkar fim sanadiyar kishin harshen Hausa , tun yana makaranta firamare yake da kishin adabin Hausa domin ya inganta harshen nasa.
Ya ce muddin mutum ya gaji harshen Hausa ya zama wajibi mutum ya yi amfani da salon Magana da azance zance a sana’arsa ta fim.
Ya ce ya fi fitowa a matsayin dattijo sannan ya fi yi fina- finan barkwanci, sannan jarumin da ya ke kalla ya ke kuma burge shi shine Ibrahim Mandawari.
Ya ce babban kalubalen da suke fuskanta dai shine rashin hadin kai daga bangaren masu fina- finai wanda a cewar sa sai da hadin kai ne za'a samu da’a a fannin fina finai.
Ko da yake burinsa ya fara shirya fina- finai da kansa tare da kiran yan uwa masu harkar fim domin su dinga fito da kayattaun fina finai.