WASHINGTON D.C+000 —
Vivian Sunday, matashiya da ta nemi karantar harkar lissafi, amma kasancewa rayuwa bata tafiya yadda aka tsara, Vivian, ta tsinci kanta a harkar kiwon lafiya.
Vivian ta ce ta shafe kimanin shekaru bakwai tana rubuta jarabbawar Jamb amma hakkar ta bata cimma nasara ba, wanda hakan ya tilasta mata mayar da hankali wajan karatun Nursing.
Ta kara da cewa kafin ta kammala karatunta sai da ta fuskanci matsaloli kafin ta kammala karatun nata , matsalolin da suka danganci harkar kudi, a cewarta sai da ta yi aiki a karkashin wata mata inda ake biyan ta naira dubu daya da dari biyar. Vivian ta ce da wannan kudi ne ta rinka tarawa tana biya wa kanta kananan bukatu.
Facebook Forum