Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Apple Zai Fitar Da Rahoton Da Ke Nuna Cinikin Wayar iphone Ya Yi Kasa


A karon farko cikin shekaru tara ana tsammanin kamfanin Apple zai fitar da rahoton da ke nuna cinikin wayar iphone yayi kasa.

Cikin tarihin kamfanin Apple wannan shine karon farko da cinikin wayar iphone yayi kasa, ana tsammanin Apple zai fitar da rahotansa da ya saba fitarwa a yau Talata.

A wata ganawa da shugaban Apple yayi da masu sharhi kan kayan fasaha ta wayar tarho ranar 27 ga watan Janairu, Tim Cook yayi gargadin cewa akwai alamun cinikin wayar iphone zai fadi warwas, wanda a tarihin kamfanin cikin shekaru 9 ba a taba gani ba.

Sai dai yayi watsi da zargin da ake na cewa yin kasa da cinikin iphone din yayi zai iya kaiwa har kaso 20 cikin 100 na cinikin kamfanin, wanda ake ganin matsalar tattalin arziki da ake fama da ita a duniya itace musabbabin rashin cinikin.

Haka kuma ana tsammamin cinikin kamfanin na wannan shekara zai kai dala Biliyan 50 ko Biliyan 53, idan aka kwatanta da cinikin kamfanin na shekarar da ta gabata Biliyan 58, tabbas za a ga na wannan shekarar yayi kasa.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG