Manyan kamfanonin Kimiya guda biyu sun fadi cewa sun kudiri aniyar daukar matakai akan kera motoci masu sarrafa kansu, don rayuwar yau da kullum.
Kamfanin motar Delphi wanda mazauninsa ke Britaniya, zai tura sabuwar motar Audi SQ5 mara rufi tafiyar kwanaki 8, wato tafiya mai nisan kilomita 5,600, daga jihar San Francisco zuwa birnin New York na Amurka, gwajin da a fara ranar 22 na wannan watan don gwada yadda motar ke tuki.
Motar dai na dauke da na’urori masu hangen nesa, masu gajeren zango kuma guda 4. Da na’urar daukar hoto guda 3, da kuma fitilu masu auna nisa da sauran dai tarkacen na’urori.
Masu sa ido akan motar zasu zauna a baya don kula da yadda motar ke tuki a kan hanya, amma zasu karbi tukin idan motar ta kauce hanya.
Wani kamfanin sarrafa kwamfuta da ke Amurka mai suna Nvidia ya fito da wata sabuwar kwamfuta da zata ba motoci masu sarrafa kansu damar koyon tuki yayinda suke kan hanya, maimakon yin tuki bisa ka’idodin da aka kera su da su.
Da wannan na’urar ta kamfanin Nvidia ne motocin zasu kware tuki kamar yadda mutane ke kwarewa ta hanyoyi daban daban yayinda suke tuki kullum.
A cikin dan lokaci, ana sa ran Kwamfutar motar zata iya gane bukatar jan burki idan wata ‘yar karamar dabba zata gitta gabanta, amma ba zata tsaya wa fallen takardar da iska ta bankado ta gabanta ba.