Wani babban matsalar dake addabar masana’antar Kannywood a wannan lokaci da muke ciki shine ta yadda mutane ke shigowa masana’antar ta bayan fagge wanda hakan ya kasance kalubale ga masana’antar.
Abdallah Tahir Alkinana mataimakin shugaban kungiyar masu shirya fina-finai na Hausa, kuma wakili na kungiyar Moppan ne ya bayyana haka a hirarsa da wakiliyar DandalinVOA.
Al kinana ya kara da cewa wannan dabi’ar na da mummunar illar ga harkar fina-finai wanda a wancan lokacin ba’a sanya kwararan matakai ba na dakile matsalolin, a yanzu kuwa an kafa kwamiti da ke zagawa duk inda ake daukar fina-finai a fadin jihar Kano domin tantancewa tare da tabbatar da cewar ba’a dauki jarumi ko jaruma a bayan fagge ba .
Ya ce duk wanda ya karya doka za’a dakatar da fim din ko kuwa ya zame wa mai fim din asara, ya kuma kara da cewa a fim din sa da mai Suna ‘Kukan Karshe’ yake yi a yanzu ya tabbatar bai sanya waka tsakani saurayi da budurwa ba kasancewar ana son kawo canji ga masana’antar fina-finai.
Inda yake cewa babban dalilan da yasa sukan sa raye-raye domin masu shirya fim sun lura masu kallonsu abu ne da suke so.