Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kar a Yi Shiru, In An Ga Wani Abu a Sanar Da Hukuma


Arewa maso gabashin Najeriya na fama da tashin hankalin ‘yan boko haram, muhimmin batun da gwamnatin Najeriya da ma makwabtan kasashenta ke kokarin ganin sun magance. Bayan kokarin da jami’an tsaro ke yi, akwai bukatar al’umma baki daya su tashi tsaye don yaki da ta’addanci a Najeriya.

Wasu shugabannan matasa, Mr. Tom Garba da Malam Kabiru Gwangwazo, a wata hira da suka yi da wakilin sashen hausa Ibrahim Abdul’aziz, sun ce ya kamata matasa su farga da lamarin ‘yan boko haram don kare al’ummarsu.

Mr. Tom ya ce, yanzu ba lokacin ne da matasa za su dinga shaye-shayen miyagun kwayoyi ba, wata babbar matsala da yawancin matasa ke fama da ita amma su dinga sa ido akan duk wani bako da ya shigo gari ko unguwa musamman a wuraren ibada, ganin yadda salon ‘yan boko haram ke canzawa.

Shi kuma Malam Kabiru ce wa yayi, yawancin lokuta ba baki kawai maharan ke amfani da su ba, don sun ja mutane da yawa cikin kungiyarsu. Ya kuma ce ya kamata iyaye su fadakar da ‘yayansu akan yadda ‘yan boko haram ke farautar wadanda zasu yi masu aiki. Shi ma ya kara da yin kira ga matasa da su sa ido sosai akan abubuwan dake wakana a unguwarnninsu.

XS
SM
MD
LG