Al’uma mazauna yankin kudancin Najeriya nata tururuwa don barin yankin zuwa Arewacin kasar. Wasu mazauna jihohin kudancin Najeriya na kara kira da babbar murya, da cewar mutane su bar barin yankin, da tunanin tashin hatsaniya a lokacin zabe.
Wasu shuwagabanin, sunyi kira da cewar mutane su yi kokarin ganin sun zauna inda sukayi katin zaben su domin kada kuri’arsu, idan kuma mutane sunyi katin su ne a Arewacin kasar to lallai ya kamata su koma don zaben shuwagabani na kwarai.
Wasu na ganin cewar wannan shine karo na farko da mutane mazauna kudancin kasar sukayi irin wannan kauran, kasancewar suna gudun wani rikici. An kuma yi kira da mutane musamman ma matasa, da su kokarta su yi zabe cikin kwanciyar hankali da lumana, matasa kada su sa kansu cikin abubuwan tarzoma.
Babban abun damuwa a nan shine idan mutane da su ka bar kudancin kasar bayan katin zabensu na kudancin yankin ne, to kaga wannan yasa baza su samu damar kada kuri'ar su ba, a dalilin haka mutane basu yi amfani da damar da aka basu ba don zaben shugabannin da zasu ja ragamar mulkin su ba.