Ranar Litinin ne aka tsare wani ’dan majalisar jihar New York tare da ‘dan sa kan laifin cin hanci da rashawa.
Shugaban masu rinjayen majalisar dattawa ta jihar New York Dean Skelos, dan shekaru 67 da ‘dan sa Adam mai shekaru 32, sun mika kansu ga hukumar bincike ta FBI, bayan da suka sami kansu cikin wata tabargaza, data hada da kwace da cin hanci da rashawa.
Wannan dai shine laifin cin hanci da rashawa na kusa kusan nan da aka sami wani ‘dan siyasa da yi.
A farkon shekarar nan ne aka bukaci wani babban ‘dan majalisa jiha da ya sauka daga kan mukamin sa, bayan da aka same shi da laifin cin hanci da rashawa.
Jami’an hukumar bincike ta FBI sunce a shekara ta 2010 an binciki shi wannan ‘dan majalisa da ‘dan sa, kan zarginsu da yin amfani da matsayin uban a gwamnati wajen neman kudi ga wasu mutanen dake harka da gwamnatin jihar. a cikin zargin harda cewa Dean Skelos yayi alkawarin gabatar da kudirin doka da zai taimaka wa manya manyan kamfani masu gina gidaje, inji FBI.
Daga baya kuma ya takurawa kamfanonin da su shirya yadda zasu biya ‘dan sa kwamishin, kan aikin da bai yi ba. har ya rinjari kamfanonin da su fara biyan ‘dan nasa Adam kudi duk wata ta hanyar yin amfani da wani kamfanin muhalli.
Mataimakin shugaban hukumar FBI Diego Rodriguez dake ofishin New York yace, “muna ‘daukar ‘yan majalisun da al’umma suka zaba da daraja, kuma zamu cigaba da kawar da cin hanci da rashawa ga duk manyan gwamnatin kasar da suka hada da karamar hukuma, jiha da gwamnatin tarayya.”