Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ko Ka San Alfanun Sana'ar Hannu - Inji Malama Fatima Sani


A shirin mu na mata, yau dandalin VOA ya sami bakuncin wata matashiya kuma mai sana’ar hannu malama Fatima Sani wadda ta kware a sana’ar dinki na maza da na mata, kuma a cewar ta, ta fara wannan sana’a ne tun kusan shekaru goma da suka gabata.

Kodashike matashiyar ta bayyana cewa ta yi gado ne wurin iyayen ta domin ainihin irin sana’ar da mahaifin ta ke yi Kenan, ta kara da cewa akwai alfanu kwarai idan sauran matasa zasu rungumi sana’ar hannu, sa’an nan kuma wadanda suke da sana’ar su yi kokarin kirkiro wasu sababbin hanyoyin inganta duk irin sana’ar da suke yi.

Malama Fatima ta ce tun daga lokacin da ta fara wannan sana’a bata taba fuskantar wani kalubalen da yasa taji bata kaunar aikin ba, sai dai ta ce babbar matsalar guda ce! Wato yadda jama’a zasu so ka biya masu bukata amma biya ya zama da wahala.

Daga karshe ta yi kira da matasa maza da mata da su mike su rungumi sana’ar hannu domin magance zaman banza da dagaro da kai, daga karshe kuma ta yi kira ga jama’a da suk rika biyan teloli idan sun yi masu aiki domin karfafa masu gwiwa su cikagaba da gudanar da ayyukan su yadda ya kamata.

Ga cikakkiyar hirar.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG