WASHINGTON, DC —
Wata kotun a Lagos, ta bada umarnin a tsare wani mutun dan shekaru 32, mai suna Tope Thomas, da ake zargi da bata wata yarinya ‘yar shekaru ukku da haihuwa a gidan wakafi.
Thomas dake zaune, a unguwar Ogba dake yanki Ikeja, makwabcin ga iyayen ita wannan yarinyar.
Dan Sanda mai gabatar da kara Sergeant Jimah Iseghede, ya fadawa kotu cewa wanda ake kara ya aikata laifin ne 28, ga watan da ya gabata a garkarsa, idan daga nan ya yaudareta.
Ya kara da cewa a lokaci da yake wannan muguwar aika aika mahaifiyar yarinyar ce ta kama shi da kanta bayan da ta ji kukar ‘yarta.
Mai Sharia Tajudeen Ellias, ya bada oda cewa a tsare Tope Thomas wanda ake tuhuma a Kirikiri har zuwa ranar 11, ga watan Nuwamba 2015.