Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Koli A Misira Zata Sake Sauraren Karar Dan Sandan Da Ya Kashe Wata Mata


Jami'an Yan Sandan Masar
Jami'an Yan Sandan Masar

Kotun kolin kasar Misira ta rushe hukuncin da aka yankewa wani Dan sanda Yassin Hatem Salah Eddin, wanda aka yanke masa hukuncin shekaru 15 a gidan wakafi bisa rawar da aka ce ya taka wajen mutuwar wata daga ckin masu zanga-zanga a farkon shekarar 2015.

Inda kotun ta bada umarnin sake dawo da sauraron karar don yin sabon hukunci. An yanke masa hukuncin ne dai a watan Yunin bara, bisa tuhumar kisan da gangan a mutuwar ‘yar gwagwarmayar nan Shaimaa el-Sabbagh mai shekaru 32 a duniya.

An harbeta ne lokacin da suke kokarin dora furanni a dandalin Tahrir, don tunawa da wadanda suka mutu a boren labarabawan Misira a shekarar 2011 da ya hambarar da gwamnatin Hosni Mubarak. A wannan lokacin ne kuma aka dankara mata harsashin da ya hallakata.

Shedun gani da ido sun ce ‘yan sanda sun hana motar daukar majinyata daga asibiti isa wajen da aka yi barin wutar kan ‘yan zanga-zangar, sannan suka hana kowa taimakawa Marigayiyar don ceto rayuwarta.

Kafar sadarwar Masar ta bayyana el-Sabbagh a matsayin mai fafutukar kare hakkin ma’aikata, kuma member ce a fitacciyar jam’iyyar hadaka a Alexandria.

XS
SM
MD
LG