Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar M4D Ta Horas Da 'Yan Mata Sama Da 150 A Jihar Kano


Kimanin mata 150 ne a kungiyar cigaban ta M4D ta yaye tare da basu kayayyakin sana’a domin dogaro da kai da kuma shirya su wajen sanin shugabanci.

Karamar hukumar dawakin tofa ce ta ci gajiyar wannan shirin inda matan yankin Gargari suka karbi wannan horo ta hannun daya daga cikin matan yankin wacce ta ke da ilimi, wato a turance mentor.

Mohd Inuwa Shu'aibu babban jam’i mai kula da harkokrin cigaba na M4D a kananan hukumomin Garin malam, Dawakin tofa da Sumaila ya bukaci matan da su yi amfani da kayayyakin da aka basu ko bayan M4D, su tabbata sun cigaba da wannan shiri don zama masu dogaro da kai.

Daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin Mariya Idris ta ce ta koyi yadda zata kashe kudinta, tare da sarrafa su game da sanin yadda mace zata rike shugabanci da koya musu sana’oi.

Ga rahoton Baraka Bashir.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:18 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG