Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lallai Wasan Brazil da Chile Zai Yi Armashi Musamman Haduwar Neymar da Alexis


Dan wasan Chile Alexis na shirin haduwa da takwaran sa Neymar na Brazil a ranar lahadi
Dan wasan Chile Alexis na shirin haduwa da takwaran sa Neymar na Brazil a ranar lahadi

Ranar lahadi mai zuwa ne Brazil zata marabci Chile a stadium din Emirates dake Ingila a wata karawa mai armashi kuma wadda jama'a da dama ke farin ciki da jiran wannan lokacin musamman ganin yadda shahararrun 'yan wasan nan wato Neymar na Brazil da kuma Alexis Sanchez na kasar Chile zasu fuskanci juna a fagen wasan cin babban kofin Copa America.

A cikin wannan watan ne tsohon zakaran dan wasan Brazil da Arsenal wato Edu Gasper yace;

"Al'amarin zai bada matukar sha'awa, ganin yadda shaharrun 'yan wasan nan Neymar da Alex zasu fuskanci juna, wato dukan 'yan wasan biyu sun kware wajan taka leda kuma abin zai bada sha'awa kwarai musamman yadda magoya bayan 'yan wasan zasu gansu suna fafatawa a lokaci guda".

Duk taurarin 'yan wasan biyu nada matukar anfani kuma su kasance masu janyo wa kasashen su yiyuwar nasara duk da banbancin nasarorin da ake ganin zasu cimma bayan gasar cin kofin duniya.

Brazil ta kasance mai takaici da mamakin ci 7 - 1 da akayi mata a wasan kusa da na karshe yayin da takwarar ta ta kasar Jamus tayi ta wasan kura da ita a fili, kuma cin yayi sanadiyyar wani mawuyacin lokaci da kawo rudani a wasan kwallon kafar na Brazil.

XS
SM
MD
LG