Sanannen dan wasan nan na kungiyar kwallon kafan Bercolona Lionel Messi dan kasar Argentina, ya karyata rahoton nan dake cewa wai zai bai taka leda don kawai kungiyar su bata samu nasarar daukar kofin COPA na Amurka ba.
Wannan mashahurin dan wasan na kungiyar ta Bercelona yasha suka daga kafafen yada labarai na cikin gida sakamakon rashin nasarar da kungiyar su bata yi na bugun daga kai sai mai tsaron gida ba.
Wannan ne yasa har wasu suka fara kiran sa da ya daina wasa haka nan.
Sai dai mai koyar da yan wasankungiyar kwallon kafa ta kasar Argentina Gerarda martino ya goyi bayan Messi din, yace kuma muddin ana zagin shi messi to ai shim aba ya tsira bane.
An jiwo shi Messin na cewa yan jarida ba zasu kashe ni ba fiye da wanda suka yi yanzun nan, kuma wadannan kalaman nasu ba sabon abu bane a gare ni.
Yace akwai wasan sada zumunta kuma muddin mai horas da ya wasa ya gayyace ni to ba tantama zan karba kiran sa.
Messi dan shekaru 28, yanzu haka dai yana cikin tawagar yan wasan da kasar Argentinan da zasu kara da kasar Bolivia da kuma Mexico wanda za ayi anan Amurka a cikin watan gobe idan ALLAH ya kaimu.