A shirinmu na wasu muhimman mata da sukataka muhimmiyar rawa a al’ummasu a yau munsamu bakunci wata matashiya Charity Hassan mai sana’ar bada man fetur a gidan mai.
Matashiyarta ce tana takardar Diplomar ta harkar tafiyar da kasuwanci watau Business Administration, ta bayyana hakan ne a wata hira da wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir.
Tace a rayuwa duk inda mutum ya samu kansaya yakamata ya godewa ubangijinsa, inda ta karada cewa rashin samun aikin gwamnati ne ya sata nemi aiki a gidan mai domin ta zamo maidogaro da kai.
Ta ce lokacin dogaro da gwamnati domin biyan bukatun mutane ya wuce tace da zarar ta tashi daga aiki a gidan mai ,tana da wata sana’ar da take yi na sayar da kayan gwanjo,a gida domin tallafawa wa iyayenta da kannanta domin su ma su sami ilimin boko .
Tace tana da burin ci gaba da karatunta, ta kara da cewa lokaci yayi da dole ne mata su tashi su nemi na kansu ko da kuwa sun yi aure a cewarta a yanzu ana lokacin da mazaje su kansu ba su ci sun koshi ba bare su bawa matansu.
Ta ja hankalin ‘yan uwanta mata da cewar, sannu da zuwa ya fi sannu da zaman gidan, duk macen da ta zauna a kan kafafunta ta saya wakanta daraja a gidan aure da zamantakewa yauda kullum.