Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahesh Bhatt: Ya Kamata Dan Adam Ya Fahimci Banbancisa Da Dabba


Mehash Bhatt
Mehash Bhatt

Kasancewar ranar malamai, mai shirya fina finai a kasar Indiya, Mahesh Bhatt, yayin da yake bayani kan wasu matsalolin da suka shafi rayuwa kamar, kunci, kisan kai, rikici tsakanin al’umma da tsana, mau’duin dake cikin fim din sa dake shirin fitowa kenan da ya yi wa lakabi da suna ‘’The Dark Side of life: Mumbai City’’ wato Bangaren rayuwa mai duhu’’, ya kamata jama'a su fahimci cewa su 'yan adam ne kafin komai.

Mahesh Bhatt, mutum ne da ake girmamawa kuma malami ne ga miliyoyin masu son shiga harkar shirya fina finai da jarumai. Yanzu kuma zai yi fitowar da ya dade bai yi irin ta ba a fim din The Dark side of Life: Mumbai City, wanda zai yi duba akan abubuwan da suka shafi rayuwa da zamantakewa.

A lokain da yake ganawa da manema labarai, ya ce: fim din zai duba, kadaicin rayuwa, hadin kan al’umma da matsalolin da suka shafi tabin hankali ta hanya mai kyau: Wani mutum Musulmi zai fara zama da wani yaro dan addinin Hindu saboda kadaici da kuncin rayuwa dake damun sa.

​Daraktan fim din ya fuskanci waddanan matsaloliln da mutane kan fuskanta na damuwa da tunani. "Ina son in issar da sakon nan ga kowa mussaman ga matasa ganin cewa ya kamata mu fahimci cewa mu mutane ne, dan haka abu na farko, ina ganin cewa hakan zai iya zama wata hanyar da zamu iya bi domin warware matsalolin da kasar mu ke fuskanta".

Ya kara da cewa a tsakiyar matsalar kashe juna da rashin imani, da rashin hadin kai da tsana, Bhatt ya ce dole ne mabiya addinin Hindu Da Musulmai su zauna lafiya don kasar ta cigaba.

Indiya na da launika da yawa, kuma daya daga cikin aunikan Kore ne, wanda shine kalar Musulmai kuma yana da alaka da kasar Indiya. Ana kashe Musulmai kuma hakan hadari ne ga kasar a cewar Bhatt. ‘’The Dark Side of Life: Mumbai City’’ , wanda Mahesh Bhatt, K. K. Menon, Nikhil Ratnarparkhi, Neha Khan da Allisha Khan kuma wanda Rajesh Pardasani ya bada Umurni kuma Tariq Khan ya Shirya, zai fito a gidajen kalo a watan Oktoba mai zuwa.

  • 16x9 Image

    Hafsat Muhammed

    Hafsat Muhammed, Ma’aikaciyar Jarida ce (International Broadcaster - Multimedia) a Sashen Hausa na Muryar Amurka dake birnin Washington, D.C.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG