Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Sana'a Biyu Maganin Mai Gasa


Aisha Sani
Aisha Sani

Aisha Sani matashiya ma’aikaciya a wani kamfanin mai zaman kansa, kuma mai sana’ar Hajja da kuma gidan abinci ta ce ta fara sana’a ne domin ta zamo mai dogaro da kai da magancen wa kanta kuncin rayuwa.

Aisha ta ce ta fara da sana’ar sayar da atamfofi ne da kayan kyalkyali na mata, daga bisani ta bude gidan abinci, a cewarta ta dade tana da shawa’ar bude gidan abinci domin ya kasance abinda take da sha’awar yin.

Ta kara da cewar duk da cewar tana aiki a kamfanin hakan ba zai hana mata yin sana’ar da ta dade tana shawa’a ba, inda ta sharwarci matasa masamman ma mata da kada su ga wani abu a matsayin cikas ga cimma burinsu.

Aisha tace tana tafiyar da sana’ar tata ne da taimakon wasu ma’aikata masu tallafa mata a gidan abinci yayin da ta ke wajen aikinta.

Ta ce babban burin ta shine ta ga cewa sana’ar ta, ta bunkasa inda take da burin barin aikin kamfanin da ta ke yi domin gudanar da sana’ar ta na kashin kanta .

Aisha ta bayyana matsalolin bashi a matsayin koma baya ga masu kananan sana’oi ta inda hakan kan jawo wa mafi yawan mutane karyar sana’a.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:51 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG