WASHINGTON DC —
Wata kotu a Abidjan babban birnin kasar Ivory Coast ta yanke wa uwargidan tsohon shugaban kasa Mr. Laurent Gbagbo, wato Mrs. Simone Gbagbo hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari, saboda wutar fitina da ta ruruta a lokacin zaben shekarar 2010 na kasar.
Malam Toure Usman wanda aka fi sani da suna Ja Ustaz, dan jaridar ne daga kasar ta Ivory Coast, yace hukuncin da kotun ta yanke, ya haddasa hayaniya tsakanin magoya bayan tsohon shugaba da sabon shugaba. Saboda sun bayyana cewa shekrun da aka yanke wa matar tsohon shugaban sun yi yawa.
To ko wannan zai zama wani darasi ga shugabanni, da matansu, da ma al’ummar kasar baki daya? Malam Toure ya tabbabatar da cewa hukuncin zai zama wani babban darasi ga al’umar kasar.