Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Man United Ta Lashe Kofin Community Shield Karo Na 20


Kungiyar kwallon kafa ta Man Utd ta samu nasarar cin kofi na Community Shield wanda ake bugawa a karshen kowace shekara kafin a fara gasar premier league, Man United ta doke takwararta Leicester City daci 2-1.

Dan wasan Man Utd mai suna Jesse Lingrad, ne ya fara jefa kwallon farko a ragar Leicester City acikin minti 32, da fara wasan inda aka tafi hutun rabin lokaci da 1-0.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, ana minti 52, da fafatawa sai dan wasan Leicester City Jamie Vardy ya rama wa kungiyar Leicester City, yayinda ya rage saura minti 7, a tashi daga wasan, sai dan wasan gaba na Man Utd Zlatan Ibrahimovic ya jefa kwallo ta biyu a ragar Leicester City.

Wannan ya ba kungiyar United damar samun nasarar daukar kofin na shekarar 2015/2016.

Shi dai wannan wasa an shirya shi ga Kungiyoyin guda biyu ne kacal.

Kungiyar da ta samu nasarar lashe kofin premier na kasar Ingila na shekarar da ta wuce da kuma nasarar data samu ta cin kofin F A Cup.

Kungiyar kwallon kafa ta Man Utd ta dauki wannan kofi sau 20 kenan tun da aka fara wasan a shekara ta 1908. Wanan shine kofin farko da Jose Mourinho ya fara ci a Kungiyar tun kama aiki da yayi a watan da ya wuce.

Haka kuma Man Utd ta bada sanarwar dan wasan kungiyar kwallon kafa na Juventus Paul pogba, yana shirin zuwa duba lafiyarsa a kungiyar ta Manchester United.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG