Yayin da shugabanni da malamai ke kira Ga gwamnati ta bude iyakokin kasar domin shigo da shinkafa daga waje, lamarin da yasa farashin shinkafa ya yi tashin gwauron zabi a kasar, manoma a jahohin kebbi da zamfara wadanda sune kan gaba wajan noman shinkafa sun bayyana cewa hakan bai dace ba.
Manoman sun bayyana cewa bai kamata a ce kasa tana dogaro da abincin da wata kasa ke nomawa ba domin kuwa a cewar su, ko Najeriya ma akan noma aka gina ta, dan haka bai kamata jama’a su cigaba da korafe korafe akan bude iyakokin kasar ba.
Daga daya bangaren kuma wasu sun bayyana ra'ayoyin su cewa manoman sun fadi haka ne a sakamakon damar da suke nema su ci Karen su ba babbaka, domin kuwa idan shinkafar da suka noma tazo, bukatarsu su yi yadda suka ga dama.
Amma kuma wasu daga cikin manoman sun bayyana cewa daukar wannan mataki yasa karfafawa jama'a gwiwa domin kuwa akwai filaye da dama da aka kwashe shekaru ba’a noma su ba amma yanzu cike suke da shinkafa.
Ga Cikakken Rahoton Murtala Faruk Daga Sokoto.