Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masassarar Dengue na iya Kisa har Lahira


Wani sabon bincike a Afrika ya yi kashedin cewa galibin cututtukan dake kawo zazzabi akan yi tunanin masassarar cizon sauro ce.

A sabon binciken da aka yi an gano cewa masassarar cizon sauro da ake kira Dengue fever a turance, dake bazuwa a wasu birane a kasar Ghana a yanzu haka, yawancin lokuta sai a yi tunanin masassarar cizon sauro ce wato malaria ke nan a turance.

Masassarar Dengue dai ana samun ta ne daga cizon wani irin sauro.

Hukumar kiwon lafiya ta duniya ta fadi cewa babu takamaiman maganin wannan cutar, amma in aka iya gano cutar da wuri aka kuma ba da kulawar da ta kamata, hakan zai rage hadarin mutuwa dake tattare da cutar.

XS
SM
MD
LG