Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Mata Ana Wanka Ko Dakile


mata
mata

A yau mun waiwayi batun nan na 'yan mata da lokacin hunturu, inda mafi akasarin ‘yan mata a wannan yanayi, kan ji gandar yin wanka akan kare, inda a wasu lokutan ma sukan shafi kwanaki ba tare da sun yi wanka ba .

Mafi akasari dai a wannan lokaci wasu ‘yan matan na gudanar da dakale, wato a wanke hannaye da kafafu da fuska da zumar sun yi wanka.

Hakkan na faruwa ne domin gujewa watsa ruwa a jiki saboda sanyin amma duk da hunturu wasu matan har sau biyu, suke wanka sabili da sun yi amanna da tsaftar jikinsu.

Masana kiwon lafiya a kowane lokaci suna kira da a tabbatar da tsaftace jiki domin yana taimakawa wajan Karin lafiya.

Akan haka ne wakiliyar dandali Baraka Bashir, ta jiyo mana ra’ayoyin wasu ‘yan mata na ko shin ana wanka akan lokaci ko kuwa ana wannan ta’adar na dakale.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:14 0:00

XS
SM
MD
LG