Kamar yadda maza ke fadi tashi a fannin kasuwanci, mata ma ba a barsu a baya ba.
Malama Hussaina Salisu Abubakar wadda ta kwashe shekaru goma sha bakwai tana sana’ar saida atamfofi, da Leshi,da kuma kayan yara, ta fadawa Dandalin VOA cewa ta fara wannan sana’ar ne saboda tana so ta sa ‘ya’yanta akan turba ta gari don ba lallai ne ilimin boko ya baka kudi ba kuma tace bukatoci sunyi yawa, dogaro ga miji ba zai yiwu ba.
Malaman makaranta da wasu na zuwa su saya su kuma dauki bashi, kuma akan bata kwangilar yin ashobin biki, karshen wata sai ta karbi kudinta.
‘Yar kasuwar dai tace babban kalubalen da take fuskanta shine, wasu zasu dauki bashi amma baza su biya ba kan kari ko kuma suyi ta yawo da hankalinta. Ta kuma ce babban burinta shine ta kara fadada kasuwancin ta kamar zuwa China don saro kayayyaki da kuma bude babban shago.
Ta kuma yi kira ga Mata da su ta tashi tsaye don barchi da zaman banza ba nasu bane, su nemi sana’ar yi don dogaro ga kai.