Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa a Najeriya Basu San Amfanin Kansu ba a Duniya


Matasa sun taru suna wakoki
Matasa sun taru suna wakoki

A yayin da zabubbukan Najeriya ke kara karatowa, wasu kungiyoyin mata da matasa, sun fara korafi game da yadda ‘yan siyasa, ke amfani dasu domin cimma burinsu amma daga bisani suyi watsi dasu.

Shugaban wata kungiyar Musulmi da Kirista, Malam Yusuf Ibrahim, yace bai gamsu da irin yadda ake amfani da matasa, a siyasar Najeriya, ba.

Yana mai cewa “ matasa a yanzu a Najeriya, basu ga amfaninsu ba a duniya, ma’ana duk abunda akeyi idan ana maganar kashe mutane, ne matasa ne ake amfani dasu, a maimakon samun matasa, a gaba-gaba wajen batun ci gabar kasa da zaman lafiya.”

Wata shugaban tallafawa mata da marayu Hajiya Hauwa Garba Kazaure, tace ta gamsu da irin rawar da aka baiwa mata su taka a Najeriya, sai dai duk da haka suna da bukatar kari.

Dama dai duk lokacin da zabe ya karato a Najeriya, ‘yan siyasa da sauran masu kwadayin ganin sun samu damar baje hajasu, sukan bude kasuwar su ta bukata domin ganin an jawo su don a tafi tare .

Mata da Matasa -3'46"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:46 0:00

XS
SM
MD
LG