Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Sun Nakadawa Wani Dan Majalisa Duka


Ginin Majalisun Tarayyar Najeriya
Ginin Majalisun Tarayyar Najeriya

Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Bosso da Paiko, a jihar Neja Salihu Adamu, ya tsallake rijiya da baya, bayan da matasan mazabar suka nakada masa duka a lokacin da ya ziyarci mazabar domin hallartar wani taro.

Wani mai ganin da ido wanda ya bukaci a sakaya sunansa yace an yaudari dan majaliisar ne da batun hallartar taro domin a cimma wannan burin.

Daga samun labarin isar dan majalisar matasan da yake dama suke kule da dan majalisar domin rashin ziyartar su tun bayan da aka zaben shi sai suka far masa da duka.

Kakakin rundunar ‘yan Sandan jihar Neja, Bala Elkana, wanda ya tabatar da afkuwar lamarin yace Sai da jami’an ‘yan Sanda suka taimaka wajen ceto dan majalisar daga hannun matasan da suke a fusace.

Ya kara da cewa abinda ya faru na harin da matasa suka kaiwa dan majalisa Salihu Adamu, yana da nasaba da siyasa kada yake yace mutane uku suna hannu. Ya ci gaba da cewa an kwantar da dan majalisar a wani asibiti a Minna wanda daga bisani aka wuce dashi garin Kaduna.

XS
SM
MD
LG