Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsayin Censorship Board Kan Sadiq Zazzbi


A yayin da hukumar tace finafinai da dabi'u ta jihar Kano ta gurfanar da mawaki Sadiq Zazzabi, gaban kuliya dangane da wata waka da ya fitar da ita ba tare da bin ka’idojin da hukumar ta gindaya masa ba dai ya bar baya da kura inda al’umma ke ta cece-kucen kan hukunci da aka yankewa mawakin.

Dandalinvoa ya samu zantawa da babban daraktan hukumar, wato Ismail mohd Na Abba dangane da kamen da akayi wa mawakin inda yake cewa laifinsa na farko dai ya sake wakar ba tare da hukumar ta bashi izini ba, baya ga gabatar da wakar gaban gungun al’umma ba tare amincewar hukumar ba

Wannan dalili ne yasa hukumar ta kai mawakin gaban kuliyar manta-sabo kan laifin da mawakin yayi, ya kuma kara da cewa babu wata siyasa a kamen da akayi wa mawakin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG