Kamfanin Microsoft ya fitar da sanarwar zai sayi shafin zumunta na Linkedin akan kudi Dala Biliyan 26.2, wanda ya zamanto babban ciniki da kamfanin ya taba yi a tarihi, kuma wani yunkurine daga shugaban Microsoft Satya Nadella, na ganin kamfanin ya ci gaba da sayar da manhajojinsa.
Wannan dai wani yunkurine da kamfanin keyi na hada hanyar sadarwar da manhajojinsa don bunkasa kasuwancinsa, yanzu haka dai akwai kimanin mutane Miliyan 433 dake amfani da shafin Linkedin.
Baki daya Linkedin da Microsoft na da alaka ‘daya, alakar kuwa itace taimakawa mutane, a cewar shugaban Microsoft Nadella alokacin da yake magana da masu fashin baki ta wayar talho.
Shi dai shafin sadarwa na Linkedin an kirkireshi ne a shekara ta 2012, aka kuma kaddamar da shi a shekara ta 2013. Kamfanin dai na samun kudin shiga da ya kai Dala Biliyan 3 a shekara, daga mutane masu neman aiki da masu daukar ma’aikata.