Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Microsoft Zai Tallafawa Matasa-1000-a Najeriya


Kamfanin Microsoft Zai tallafawa matasa 1000 a Najeriya.
Kamfanin Microsoft Zai tallafawa matasa 1000 a Najeriya.

Shahararren kamfanin yin manhajar komfutar nan na Microsoft, ya kaddamar da shirin samar da ayyukan yi ga matasa na CloudPreneur Initiative a Najeriya, da zummar samar da ayyukan yi ga matasan Najeriya akalla 1,000 a tashi guda, wadanda za su zama masu saida manhajoji da sauran kayan cloud a Najeriya.

Tuni aka shawarci matasan Najeriya su yi rajistar nemar aikin a dandalin Cloud. Baya ga samar da ayyukan yi ga matasan, shirin na CloudPreneur Initiative zai kuma karfafa gwiwar matasa masu kwazo a fannin fasaha.

Shugabar Fate Foundation a Najeriya Habiba Balogun ta ce shirin zai rage fatara ya kuma samar da dukiya tsakanin matasan Najeriya.

Shi ma shugaban Mara Mentor Hetal Shah, ya ce suna masu farin cikin shiga shirin na Cloudpreneur a Najeriya.

Matsalar rashin ayyukan yi ga matasa na daga cikin manyan ababan da ke sa su shiga ayyuka marasa kyau kamar shaye-shaye da sauransu.

XS
SM
MD
LG