Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mikel Obi Na Son Kafa Makarantar Kwallon Kafa


Gwamnan jahar Neja, Abubakar Sani Bello, na sha suka daga al’umar jahar saboda zuwa kasar Ingila, da yayi kallon wasan kwallon kafa tsakanin Chelsea da Arsenal, a asabar din da ta gabata, ganin rashin kudi da jahar ke fama da ita.

A bayanin da Gwamnan yayi a shafin sa na sada zumunta na Twitter, yace ya je kasar Ingila, ne a bisa gyayyatar dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa na Chelsea, Mikel Obi, wanda ke son kafa makarantar koyon wasan kwallon kafa a jahar Neja.

Mikel Obi, yace tuntubar Gwamnatin jahar da ya yi domin hada hannu da ita a bunkasa harkar wasan kwallon kafa abun ne mai kyau kuma ba zai kyautu ace Gwamnati tayi burus da irin wannan hubbasa ba.

Mai taimakawa Gwamnan ta fuskar labarai, Dr. Ibraheem Dooba, yace duk da yake tafiyar ta Gwamna a bisa gyayatar Mike Obi, ne Gwamnan zai sadu da wasu wadan da zasu iya saka jari wajan batun kafa matarantar wasan kwallon.

XS
SM
MD
LG