WASHINGTON DC —
A yau ma mun sake samun bakunci wani mawaki wanda ya ce tun bayan lokacin da na ziyarci dandalin VOA,
Na samu cigaba da dama, daga ciki har da canza salon waka ta daga hip hop zuwa fasalin irin salon wakokin da ake ji a yanzu, wato salo na Afro-pop kamar yadda mawaki Fela Kuti ke yi a da...
A ta bakin mawaki, Bashir Idris wanda aka fi sani da Mixter Bash, Mr. More music more sauti mai daban daban.
Ya ce dole ne mawaka su saje da yadda zamani ke tafiya, sabanin yadda yake yi a da na zube, a yanzu kuwa yana waka ce a zube cikin sanyi ba tare da sauri ba.
Mixter Bash ya ce a yanzu ne yake amsa sunan sa na Limamin sauti, mai daban daban kamar Fantimoti.
Ya ce wakokinsa suna fadakarwa ne na cewar matasa masu waka su daina dogara akan waka kadai, lallai su nemi sana’o'in dogaro da kai.
Ya kara da cewar kasancewa shi mawaki hakan bai sa ya dogara da waka kadai ba, yana noma sannan yana aikin da ake biyansa albashi.
Facebook Forum